1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelenskiy ya koka da rarrabuwar EU kan Rasha

Abdul-raheem Hassan
May 27, 2022

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya nuna takaici kan yadda kungiyar Tarayyar Turai ke kokarin cimma matsaya kan sabon takunkumin da ta kakaba wa Rasha.

Ukraine | Präsident Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Ukraine Presidency/ZUMA Press/IMAGO

Shugaba Zelensky ya sake nanata cewa kasashen duniya sun gaza mai da tsarin bankin Rasha saniyar ware, ya kuma zargi kasashen yamamcin duniya da jan kafa na samar wa Ukraine manyan makamai.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar EU ke tattaunawa karo na shida kan matakai na gaba a kan takunmumin ciki har da takunkumin hana shigo da mai na Rasha.

Yanzu haka dai rahotanni daga gabashin Ukraine, na cewa sojojin Rasha sun kashe akalla mutane 1,500 tare da lalata kusan kashi 60 na gidaje. Sai dai Shugaba Putin ya ce bai shiga Ukraine don mamaye yanki ba, sai don rage karfin sojanta.