1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky ya yaba wa EU kan ladabtar da Rasha

Abdul-raheem Hassan MAB
June 1, 2022

Shugaban kasar Ukraine ya yi kira da a duba yiwuwar tsari na bakwai na takunkumin EU a kan kasar Rasha bayan cimma matsaya kan tsari na shida, yana mai bayyana Rasha a matsayin ‘yar ta’adda.

Kiew PK Selenskyj Duda
Hoto: Efrem Lukatsky/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gode wa Kungiyar Tarayyar Turai EU kan shirinta na shida da ya cimma mastayar kara wa kasar Rasha takunkumin hana sayan man feturta.

Duk da cewa Amirka ta yi barazanar tura wa Ukraine samfurin makaman roka na zamani, amma Shugaba Zelensky ya bukaci kasashen yamma su kara wa Rasha takunkumi na bakwai, inda ya kwatanta Rasha da 'yar ta'adda.

Yanzu haka dai, Asusun Kula da Kananan Yara na MDD Unicef ya ce fiye da yara miliyan biyar a Ukraine na cikin wani hali saboda tsananin yaki.