1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelensky ya yi kiran zanga-zanga ta duniya

March 24, 2022

A cikin wani jawabi na Ingilishi da Zelenskyy ya yi na bidiyo a ranar Laraba ya ce hakan ya zama wajibi a kokarin da kasar ke yi na bijire wa kutsen Rasha.

Russland Ukraine Krieg | Wolodymyr Selenskyj
Hoto: Ukrainian Presidential Press Office via AP/picture alliance

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi kira ga 'yan kasarsa mazauna ketare da su fito su yi zanga-zangar adawa da mamayar da Rasha ke yi wa kasarsa. Shugaban ya ce ta haka ne duniya za ta gane girman matsalar, kuma kasashe su sanya hannu wurin dakatar da kutsen na Rasha.

Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnatin Burtaniya ta ce za ta tura wa Ukraine tallafin makamai masu linzami 6,000 domin kare kanta daga dakarun Rasha. Sai dai kuma wasu bayanan sirri da kasashen Yamma ke fitarwa na cewa dakarun Rasha sun yi cirko-cirko a nisan kilomita 15 zuwa 20 da birnin Kiev na Ukraine, kuma tirjiyar da suke ci gaba da fuskanta ce ta dakile aniyarsu ta fada ma fadar gwamnatin Ukraine din a cikin makonni hudu da aka kwashe ana barin wata.

A wannan Alhamis kungiyar tsaro ta NATO ke gudunar da taro na gaggawa a kan rikicin Rashan da Ukraine. Shugaba Joe Biden na Amirka na cikin wadanda za su yi jawabi a taron da ke da zummar lalubo hanyoyin yadda kasashen Yamma za su yi da Shugaba Putin na Rasha.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani