1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelenskyy: Diflomasiyya ce mafita a tsakaninmu da Rasha

May 22, 2022

Yayin da kasashen yamma ke ci gaba da bai wa Ukraine tallafin kudade da makamai, shugaban kasar ya ce matakan diflomasiyya ne zai kawo karshen takaddamarsu da Rasha.

Ukraine Kiew | Pressekonferenz: Charles Michel und Wolodymyr Selenskyj
Hoto: VALENTYN OGIRENKO/REUTERS

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine, ya ce matakin diflomasiyya ne kadai zai iya warware matsalar da ke tsakanin kasarsa da Rasha ba kuma karfin soja kadai ba.

A jawabin da ya gabatar a ranar Asabar, Shugaba Zelenskyy ya kuma nuna bukatar shigar da Ukraine cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Jawabin nasa ya zo ne yayin da Amirka ta amince da bai wa kasar dala biliyan 40 a matsayin tallafi saboda yakin da take fama da shi.

Kawayen Ukraine na yammacin duniya dai na ci gaba da bai wa kasar tallafin makaman yaki ne tare da kakaba manyan takunkuman karya tattalin arziki kan Rasha.

Shugaba Zelenskyy ya ce wasu batutuwan na bukatar zama kan teburi ne, ba kuma tsananin amfani da karfin wuta daga tsinin bindiga ba.

A halin da ake ciki dai Rasha ta ce ta yi nasarar lalata wani tarin makamai, wadanda kasashen Turai da Amurka suka aika wa Ukraine a yankin arewa maso yammacin kasar.