Zida na yunkurin bai wa fararen hula iko
November 15, 2014Shugaban sojin rikon kwaryar Burkina Faso, ya ce ya maido da kundin tsarin mulkin da aka dakatar bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore sakamakon zanga-zangar al'umma.
Leftanant Kanar Isaac Zida wanda ya aiyana kansa a matsayin shugaban kasar ranar daya ga watan Nuwamba, ya ce ya kuma bai wa jagororin siyasar kasar daga yau zuwa ranar Lahadi su fitar da sunayen wadanda za a iya zaba, su maye gurbin shugaban da zai jagoranci kasar kafin zabe.
Da ma dai Kungiyar Tarayyar Afirka ta bai wa Zida wa'adin makonni biyu ya mika mukamin rikon ga fararen hula ko kuma ta kakaba mi shi takunkumi.
A ranar Lahadi sojojin kasar, da jam'iyyun siyasa, da fararen hula da shuwagabannin addini za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta bayar da suffar yadda gwamnatin rikon za ta kasance. Bisa tanadin wannan yarjejeniya, kwamitin da zai zabi shugaban kasa ya hada da sojoji biyar, 'yan adawa biyar, na hannun daman tsohon shugaban kasa biyar da kuma fararen hula da wakilan addinan kasar su takwas. Bayan an zabi wannan shugaban, ba zai iya tsayawa takara a zabuka masu zuwa ba, sai dai yana da izinin zaban sabon Firaminista, wanda shi kuma zai zabi majalisar ministocin da ya kunshi mambobi 25.