1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Shugaba Robert Mugabe ya yi murabus

Gazali Abdou Tasawa MNA
November 21, 2017

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin kasar ta soma zama domin tsige shi bayan da ya ki sauka daga mulki duk da kiraye-kirayen da yake samu daga bangarorin al'ummar kasar ta yin hakan.

Simbabwe Mugabe bei TV-Ansprache
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Shugaban majalisar dokokin kasar Zimbabuwe Jacob Mudenda ya karanto takardar murabus da Shugaba Mugabe ya aika wa majalisar domin sanar da yin murabus dinsa daga karagar mulkin kasar. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da majalsar ta fara wani zama a wannan Talata domin tsige shugaban mai shekaru 93 da kuma ya kwashe shekaru 37 a kan kagarar mulkin kasar ta Zimbabuwe.

Yanzu haka dai matakin shugaban na yar da kwallon mangwaro ya sanya majalisar dokokin kasar ta Zimbabuwe ta dakatar nan take shirinta na tsige shugaban. Kuma tuni 'yan majalisar dokokin suka bayyana farin cikinsu da wannan lamari, kamar yadda wadannan 'yan majalisa suka nunar.

Murna da sowa sun barke a majalisar dokoki bayan samun labarin murabus din MugabeHoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

"Ban yi mamaki da abun da ya faru ba wannan abu na faruwa tun makwanni biyu da suka gabata. Sai dai yanzu komai ya zo karshe, abin da zan ce kawai shi ne wannan mutum ne da ya yi abubuwa da yawa a kasar nan yana neman hutu, ya kamata da ya dau wannan matakin tun farko, ya yi abun da zai fisshe shi, abu mai muhimmanci yanzu shi ne hadin kan kasarmu."

"Wannan abin tarihi ne, akwai abin da za mu koya a kan abin da ya faru tare da yin gyara a inda muka yi kuskure domin kara bunkasa kasarmu. Yanzu shugaban ya nuna damuwa kan zaman lafiya da kwanciyar hankalinmu, 'yan kasa su ma suna nuna damuwa a kan wannan yanzu kuma mun samu dama za mu ciyar da kasarmu gaba."

Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Dubunnan jama'ar kasar ta Zimbabuwe sun fantsama a saman titunan biranen kasar jim kadan bayan sanar da murabus din Shugaba Mugabe. Kuma da dama daga cikinsu sun bayyana fatan kyakkyawar makoma ga kasar tasu kamar dai yadda wannan mata daga cikin masu zanga-zangar ke nuna farin cikin take cewa:

"Muna kyautata zaton samun makoma mai kyau, mai haske ga kasarmu domin Allah ya huwace mana arziki na karkashin kasa wanda ka isa sa mu kasance a sahun gaban kasashen da suka ci gaba a duniya, muna da kuma kasar noma mai albarka, ga masu ilimi da suka san makamar aiki kana mutanen kasar nan suna da juriya a fagen aiki."

Sai dai kamar yadda malam bahaushe ke cewa wai ko wani allazi da nashi amanu, domin kuwa a daidai lokacin da 'yan kasar ta Zimbabuwe da dama suka dawo daga rakiyar Shugaba Mugabe tare ma da juya masa baya, har yanzu akwai wasu da ke ci gaba da begensa. Lawrence Chingwaru wani matashi mazaunin birin Harare na daga cikin masu goyon bayan shugaban mai tsawon shekaru.

"Lalle ya tsufa amma mu har yanzu muna kaunarsa domin iyayenmu sun bamu labarin gwagwarmayar da ya yi a shekarun baya. Lalle ya dade yana shugabancinmu, amma ni dai ban ga wani laifi a tare da wannan mutum ba."

Sai dai kuma daura da haka kungiyar kasashen Kudancin Afirka ta SADC ta sanar shirin aika wata tawagar shugabannin kasashen yankin da suka hada da Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da Joao Louenco na Angola zuwa kasar ta Zimbabuwe a wannan Laraba domin gane wa idanunsu abin da ke faruwa a kasar.