1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe ta samu nasarar dakile maleriya

Privileg Msvanhiri/Yusuf BalaApril 25, 2016

Kasar Zimbabuwe dai ta yunkura wajen yaki da wannan cuta ta zazzabin cizon sauro inda ya zuwa yanzu ake samun ci gaba ta wannan fanni.

Malariamücke Malaria Fiebermücke
Hoto: picture-alliance/dpa/Wildlife/W.Moeller

Kamar sauran kasashe a duniya kasar ta Zimbabuwe na kokari wajen ganin ta kawar da cutar ta maleriya, kuma ya zuwa yanzu kasar ta samu ci gaba sosai ganin yadda wadanda suke kamuwa da cutar suka ragu yayin da a hannu guda kuma mutuwa ta sanadin cutar aka samu sauki sosai.

A farkon shekarun 2000 kasar ta Zimbabuwe tana yin rijistar mutane da suka kamu da cutar ta zazzabin cizon sauro na maleriya miliyan biyu a kowace shekara, yayin da ake samun mutane 5,000 na mutuwa, amma yanzu ana samun kasa da dubu 500 ne a shekara ke kamuwa da cutar yayin da masu rasuwa ke zama 350. Abin da ke da nasaba da kulawa da fannin yaki da cutar ya samu daga gwamnatin kasar.

Hoto: DW/P. Musvanh

Gadzirai Mateme jami'i mai kula da marasa lafiya a asibitin Gache Gache a garin Kariba wanda ke da tazarar kilo-mita 360 daga birnin Harare fadar gwamnatin kasar ya ce an samu ci gaba da yaki da cutar kuma yayin damina ke kunno kai za su kara himma.

Shirin Roll Back Malaria a shekarar 2000 dai ya kai ga jama'a da ke zaune kauyika dauki a kasar ta Zimbabuwe alal misali a garin Kariba da ke kusa da tafkin Kariba wanda shi ne ruwan da ake amfani da shi wajen samar da hasken wutar lantarki a Zimbabuwe

Kokari dai na kawo karshen cutar ta maleriya a Zimbabuwe na haduwa da cikas kamar nisa zuwa wasu kauyika, wani lokaci jami'an lafiya kan yi amfani da kwale-kwale a ratsa tafki dan kai wa ga marasa lafiya a garin Kariba, kamar yadda Gadzirai Mateme ke cewa.

Hoto: getty / T. Karumba

Duk da wannan kalubale kasar ta Zimbabuwe na da buri na ganin ta kawar da cutar ta zazzabin cizon sauro ko maleriya nan da shekara ta 2020.

Gwamnati dai ta yi tsari kan yaki da cutar wadda ake nazari duk bayan shekaru biyar domin sanin ci gaba da aka samu. A shekarar 2012 an ga sakamakon nazarin aikin haka akwai rahoton da zai fita a 2016.