Zimbabuwe: Diyya ga manoma farar fata
April 23, 2025
An shafe shekaru sama da ashirin ana musayar yawu tsakanin gwamnati da manoma fararen fata a Zimbabwe kan gonakinsu da gwamnati ta kwace a wancan lokacin tare da mika su ga yan kasa bakaken fata a shekara ta 2000. To sai tsarin da gwamnatin ta bujiro da shi bai yi wa manonan dadi ba kasancewar za su shafe shekaru da dama kafin samun hakkokinsu, duk da cewa ministan kudi na kasar Mthuli Ncube ya kare matsayar gwamnati, inda ya ce sun biya manoma 378 daga cikin 700 da aka rattaba hannu da su kan yarjejeniyar 2020.
"Ya ce, a yarjejeniyar da aka cimma shi ne zamu biya wani kaso na kudin, wato kashi 1% na abin da kowanne manomi ke bi, sannan kuma kashi 99% za a biya su da dalar Amurka a cikin shekaru 10. A don haka mun fara wannan shiri kuma mun biya dala miliyan $3.1.
To amma me manoman Harare fararen fata ke cewa game da furucin ministan kan biyansu hakkokinsu?
"Guda daga cikin shugabannin manoman fararen fata Deon Theron da ke cewa manoman sun yi fatali da wannan bukata, duba da cewa yawancin mu mun kai shekaru 70 zuwa 80, yaushe zamu amfana da jingar shekara 10, ai ba abin da zamu samu.
Tun bayan kwace gonakin manoma fararen fata, hukumomin kasa da kasa da bankunan lamuni suka lafta wa Zimbabwe takunkumai, wanda ya kai ga durkushewar tattalin arzikin kasar. To ko me ya sanya manoman karbar kashi 1% bisa 100, duk da adawa da suke yi matakin?
"Ya ce, muna ta fadi tashin samun abin da za mu ci. Muna fama da matsaloli na rashin lafiya kuma ba zamu iya dawainiyar kula da lafiyarmu ba. A don haka manoma basu da zabi illa karbar wannan kudi da bai taka kara ya karya ba.
Wani masanin tattalin arziki a Zimbabwe Prosper Chitambara ya ce basukan da kasashen duniya ke bin kasar na sama da dala biliyan $21 ya sanya ta cikin wadi na tsaka mai wuya.
"Ya ce, gwamnati ta bada damar biyan wadannan manoma. Idan ka kalli tattalin arzikin kasar mu, kwanan nan muka farfado daga matsalar fari. Kusan tattalin arzikin kasar na durkushewa sannu a hankali.
Batun mallakar kasa ko filin noma tsakanin fararen fata da kuma bakake na ci gaba haifar da rikici a kasashen kudancin Afirka tun bayan mulkin mallaka.
Shugaba Emmerson Mnangagwa wanda ya hau karagar mulki bayan saukar Mugabe daga shugabancin kasar sakamakon matsin lamba, yana ci gaba da yaukaka dangantaka da kasashen Turai tare kuma da fadi tashin ganin an yafe wa Zimbabwe dimbin basukan da hukumomin lamuni ke bin ta musamman IMF.