Ziyara A. Merkel a Asia
August 27, 2007Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel, ta fara rangadi kwanaki 6 a nahiyar Asia.
Merkel ta kai wannan rangadi da riga 2, na farko a matsayin ta, na shugabar ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a turai, sai kuma na 2, a matsayin ta, na shugabar rukunin ƙasashe 8 masu ƙarfin tattalin arziki a dunia.
Mahimman batutuwan da ke ajendar wannan ziyara, sun haɗa da harakokin cinikaya, sai kuma batun yaƙi da gubatar yanayi.
Kazalika, Angeller Merkell,zata tanttana da hukumomin Sin, a game da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan, ta la´akari da goyan bayan da Pekin ke baiwa Sudan.
Jim kaɗan bayan fara wannan rangadi, Merkell ta bayyana batutuwan da ke tafe da ita:
Kowa ya san da cewar Asia, yanki ne, mai muhimmanci, ta fannin tattalin arziki.
A matsayi na, na shugabar ƙasashen G8 ,za ni anfani da wannnan dama, domin yin bitar hulɗoɗi tsakanin Asia da ƙasashen na G8.
Za ni ziyarci Sin da Japon, a ƙasar Sin, za mu tantana da hukumomi, albarkacin cikwan shekaru 35, da ƙulla mu´amila tsakanin Jamus, da ƙasar.
A tsawan wannan lokaci, mun cimma nasarori masu yawa, ta fannonin saye da sayarwa da kuma al´adu.