Ziyara Angela Merkel a Amirika
November 9, 2007Nan gaba a yau ne, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, zata gana da shugaban ƙasar Amurika Georges Bush a gidan gonar sa, da ke Jihar Texas.
Ziyara ta Merkel a Amirika, na wakana kwanaki 2 bayan da shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy ya kammala ta sa.
Bush da Merkel za su tantana a kann batutuwa dabam-dabam, mussamman rikicin nuklear ƙasar Iran, da kuma halin da ake ciki a ƙasar Afghanistan.
A na fuskantar saɓanin ra´ayoyi tsakanin Amirika da Jamus, a game da wannan batutuwa.
Jamus ta bayyana adawa da manufar Amirika, ta yi anfani da karfin bindiga a kann Iran , sannan hukumomin Berlin hau kujera na ƙi, akan buƙatar Amirika ta ƙara yawan sojojin Jamus a Afghanistan.
A ɗaya wajen shugabanin 2, za su masanyar ra´ayoyi a game da rikicin ƙasashen Burma da Lebanon da dai sauran batutuwa da su ka shafi mu´amila a tsakanin su.