1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice Turquia

April 25, 2006

Yau ne sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta fara ziyara aiki a ƙasar Turquia.

Rice zata gana da takwaran ta na Turquia, Abdullah Gul da Praminsita, Recep Tayib Erdogan , kamin ta gana da shugaban ƙasa Ahmet Necdet Sezer, gobe idan Allah ya kai mu.

Za su tantana a kan batutuwa daban daban ,da su ka shafi rikicin ƙasar Saipros ko kuma Chypre,da matsalar yan awaren ƙurdawa na PKK.

A jajibirin wannan ziyara, Turquia, ta nemi taimako, daga Amurika, ta fannin masanyar rahotanin sirri, da kayan aiki, domin yaƙar yan awaren ƙurdawa da wasun su,su ka girka sanssani a arewancin ƙasar Irak.

Wannan ƙungiya na matasayin babbar barazana, ga kwanciyar hankali a ƙasar Turquia.

Condolseesa Rice na kammala wannan ziyara gobe laraba.