1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Koffi Annan a Japan

May 16, 2006

Sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, ya kai ziyara aiki a ƙasar Japon.

A tswan wannan rangadi na kwanaki 3, Annan zai tantana da hukumomin Tokyo, a game da batu kwaskwarima ga dokokin Majalisar Ɗinkin Dunia.

Koffi Annan da wa´adin mulkin sa ke kai ƙarshe, a watan desember na wannan shekara, na bukatar gudanar da kwaskarima ga dokokin Majalisar, kamin ya bar mukamnin na sa.

Ƙasar Japon, ke riƙe da matsayi na 2, bayan Amurika, ta fannin bada kuɗaɗe ga Majalisar Ɗinkin Dunia.

Japon ta yi barazanar rage yawan kuɗaɗen da ta ke badawa, muddun ta kasa samun kujerar dindindin, a komitin sulhu, na Majalisar Dinkin Dunia.

Bayan ƙasar Japon, Koffi Annan, zai ziyarci China, Vietnam, da kuma Thailand.