1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugaba Ely Ould Mohamed Vall a Spain

October 31, 2006

Shugaban ƙasar Mauritania, Ely Ould Mohamed Vall, ya kammalla ziyara aikin kwanaki 2, da ya kai a Spain,inda ya ganan da shugaban gwamnati, Jose Louis Rodrigez Zapatero.

Magabatan 2, sun yi anfani da wannan dama,inda su ka tantana akan makomar siyasar Mauritania, da kuma matsalar baƙin haure.

Shugaba Mohamed Vall, ya tabbatar cewa, gwamnatin sa tayi nisa, wajen tsare-tsaren zaɓen shugaban ƙasa, da za ayi, a watan maris mai zuwa.

A ɓangaren yaƙi da kwarara baƙin haure, Spain ta yi kyaukyawan yabo ,ga hukumomin Nouwakshot,a game da kokarin da su ke ta wannan fannin.

A sakamakon gama ƙarfin ƙasashen 2, sun yi cimma nasara taka birki, ga a ƙalla bakin haure dubu 11, daga wannan shekara zuwa yanzu.

Sannan sun bayyana daukar sabin matakai, na haramta wananbaki anfani da gabar tekun Mauritania, domin shiga Spain, ta ɓarauniyar hanya.