Ziyara shugaba Hu Jintao na China a Vietnam
October 31, 2005Talla
Shugaban kasar China Hijintao ya sauka sahiyar yau a birnin Hanoi na Vietnam a wata ziyara aiki ta kwanaki 3.
Wannan itace ziyara ta farko da shugaban ya kai a Vietnam a matsayin sa na shugaban kasa.
Kasashen 2 za su anfani da wannan dama, domin karfafa mu´amilar cinikaya tsakanin su, da kuma kara daidaita diplomatia.
China da Vietnam sun samu rashin fahintar juna a shekara ta 1979 bayan da China ta kai hari ga Vietanam, dalili da mamayar da ta yi wa Kambojiya.