1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Vladmir Putine a Kasar Holland

November 2, 2005

Shugaban Rasha Vladmir Putine ya kai ziyara a kasar Holand.

A dganawar da yayi da magabatan wanan kasa sun tantana a akn batutuwa daban daban da su ka shafi harakokin diplomatia tsakanin su.

Hassali ma maganar yaki da ta´adanci da huldodin cinikaya.

A taron manema labarai da ya yi, Vladmir Poutine, ya bayyana gamsuwa da wannan ziyara, da kuma daidaiton da su ka cimma da hukumomin la Haye, kokuma The Hage a kan dukan batutuwan da su ka tantana a kai.

A nasa bangare, shugaban gwamnatin Holland Jean Peter balkenende ,ya tabo batun masu fafatakar kare hakokin bani adama, na Ceceniya, inda ya bukaci shugaban na Rasha, ya dubi wannan matsala da idon rahama.

Matsalar Ceceniya, na daya daga ababen da su ka gurbarta dangata tsakanin Rasha da kasar Holland a shekara da ta gabata.