1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar al-Bashir na Sudan a China

June 29, 2011

Kasar China ta rungumi shugaba Omar al-Bashir da hannu biyu yayin saukarsa a China duk kuwa da sammacen kama shi bisa laifukan yaki a yammacin kasarsa

Shuga Hu Jintao(dama) da Omar al-Bashir a Babban Zauren Kasar ChinaHoto: AP

Shugaba Omar Hasan al-Bashir na Sudan ya samu gagarumar tarya daga shugaba Hu Jintao yayin saukarsa a kasar China. Shugaban na Sudan ya samu wannan taryar ne duk da kuwa sammacen da kotun hukunta miyagun laifuka ta kasa da kasa ta bayar akansa bisa aikata laifukan yaki a yammacin kasarsa Sudan. Hu ya ce zai ci gaba da zartar da manufofin kyautata dangantakar kasarsa da Sudan ba ma tare da yin la'akari da sauye-sauyen da ake samu a duniya da kuma ci gaban da ake samu a kasar ta Sudan ba.

Kasar China dai ita ce ke sahun gaba a cinikin makamai da man fetur da kasar Sudan. Harabobin man fetur na kasar ta Sudan ana samunsu ne a kudancin kasar da ke shirin ballewar a ranar 9 ga watan Yuli. Fatan China dai shine tabbatar da cewa ballewar kudanci ba za ta janyo rikicin da ka iya zama karen tsaye ga bukatun da take da su gun bangarorin biyu ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal