Ziyarar Angela Merkel a Afirka
July 11, 2011A yau ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fara wata ziyarar ran gadi a ƙasashen Afirka guda uku tare da shugabanin manyan kamfanonin nan Jamus. Ƙasashen da za ta ziyararta sun haɗa da Kenya, da Angola da kuma Najeriya. A wani jawabi da ta yi a ƙarshen makon da ya gabata, Merkel ta ce Jamus na buƙatar ƙulla ƙawance da Afirka a fanin makamashi, musamman ma irin makamashin da ake sabuntawa. Ƙasashen uku dai na daga cikin ƙasashen nahiyar da suka fi amfani da nauororin da Jamus ke sarrafawa. Wannan ziyara ta Merkel wadda za ta faro daga Kenya na zuwa ne wata ɗaya daidai bayan da gwamnatin a birnin Berlin ta ƙaddamar da sabbin manufofinta dangane da Afirka waɗanda ke mayar da hankali wajen ƙulla ƙawance a fanin tattalin arziƙi da ƙasashen a maimakon bada tallafi kawai
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Abdullahi Tanko Bala