1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikicePakistan

Iran: Ziyarar babban jami'in tsaron Pakistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 22, 2026

Hafsan hafsoshin Pakistan Field Marshal Asim Munir na kan hanyarsa ta zuwa ziyarar aiki Iran, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Pakistan | Ziyara | Iran | Field Marshal Asim Munir
Babban hafsan hafsoshin tsaron Pakistan, Field Marshal Asim Munir Hoto: Pakistan's Inter-Services Public Relations (ISPR)/AFP

Pakistan da ke zaman makwabciya kana kawa ga Tehran, ta jima tana kokarin shiga tsakanin da nufin kawo karshen yakin da Iran din ke fafatawa da kasashen Amurka da Isra'ila. A nasa ran Field Marshal Asim Munir zai gana da shugabannin Iran yayin ziyarar tasa, wadda ke zuwa a daidai lokacin da Tehran ke yin nazarin sababbin sharuddan Amurka na kawo karshen yakin na yankin Gabas ta Tsakiya.