1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR CONDOLEEZA RICE A GABAS TA TSAKIYA

Yahaya AhmedFebruary 7, 2005

A farkon ziyararta a Gabas Ta Tsakiya tamkar sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta kyautata zaton cewa, za a cim ma zaman lafiya mai dorewa a yankin gaba daya.

Condoleeza Rice, sakatariyar harkokin wajen Amirka.
Condoleeza Rice, sakatariyar harkokin wajen Amirka.Hoto: AP

A yayin da ta sauka a birnin Kudus, Condoleeza Rice, sabuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka, wadda take kai ziyararta ta farko a Gabas Ta Tsakiya, tun da aka nada ta a wannan mukamin, ta ce halin da ake ciki yanzu a yankin na ba da wata dama, wadda ya kamata a yi amfani da ita wajen cim ma zaman lafiya. Ta kuma yabi sabon shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, wanda ta ce matakan da ya dauka tun da aka zabe shi, za su iya farfado da komawa ga teburin shawarwari don aiwatad da shirin nan na daftarin zaman lafiya, wanda Amirka ta jagoranci tsarawa. Dole ne dai, inji ta, Isra’ila ta yanke wasu shawarwari, wadanda duk da cewa ba za su farantar wa bangarori da dama na kasar rai ba, za su taimaka wajen samad da zaman lafiya da kuma kafa kasar Falasdinawa mai `yancin kanta, a yankin na Gabas Ta Tsakiya.

Rice, ta kawo ziyararta ne dab da wani taron kolin da za a yi a kasar Masar, tsakanin Firamiyan Isra’ilan Ariel Sharon da shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas. A gobe talata ne dai shugabannin biyu za su gana da juna a karo na farko, tun da Abbas ya hau mukamin shugaban Falasdinawa, a gun yawon shakatawar nan na Sharm-el-Sheikh a kasar Masar. Yayin da ta gana da Firamiya Ariel Sharon a birnin kudus, Rice ta bayyana cewa:-

"Gwamnatin Amirka ta gamsu da cewar za ka sadu da Abbas a birnin Al-bahira. Wannan dai wani lokaci ne na fata, amma kuma wani lokaci na daukar nauyin da ya rataya a wuyarmu, mu duka, wato na nuna misali a zahiri da aiwatad da duk ababan da muka yarje a kansu."

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ne dai, ya gayyaci shugabannin Falasdinawan da na Isra’ila zuwa taron kolin. Sarki Abdallah na Jordan ma zai halarci wannan taron. Duk bangarorin biyu, wato Isra’ila da Falasdinawa, na kyautata zaton cewa, ganawar da shugabanninsu za su yi, za ta haifad da sakamakon kulla wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninsu.

Wasu masharhanta dai na ganin cewa, ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amirkan, sanya wata alama ce da nuna wa abokan huldar Amirkan a Turai cewa, har ila yau dai ita Amirkan ce ke jan akalar al’amura a yankin na Gabas Ta Tsakiya. A cikin jawabin da ya yi kan matsayin kasarsa a kwanakin baya, shugaba Geoge Bush na Amirka, ya bayyana cewa, an kusa cim ma gurin wanzuwar kasashe biyu, wato Isra’ila da Falasdinu, masu bin tafarkin dimukradiyya, wadanda kuma ke zaune tamkar makawbatan juna cikin lumana, a yankin na Gabas Ta Tsakiya. Shugaban na Amirka dai, ya ba sanarwar bai wa Falasdinawan taimamkon kudi na kimanin dola miliyan dari 3 da 50. Amma kuma har ila yau, Isra’ilan za ta ci moriyar kusan dola miliyan 80 daga wannan kudin, don gina tashoshin iyaka, a katangar nan da take ginawa tsakaninta da yankunan Falasdinawan a Gabar Yamma.

A ziyarar da ta kai a birnin London a ran juma’ar da ta wuce, Rice ta bayyana cewa, a shirye kasarta take ta ba da taimako wajen horad da jami’an tsaron Falasdinawa.

Wasu bangarorin gwamnatin Isra’ilan dai na nuna damuwarsu ga ziyarar Rice a yankin. Da farko, ganin yadda Abbas ke samun karbuwa a Washington, na kara bata wa wasu jami’an Isra’ilan rai. Suna dai farrgabar cewa, Falasdinawan za su iya yin amfani da wannan damar ne wajen angaza wa Rice, da ta kare maslaharsu a tattaunawar da za ta yi da shugabannin kasar bani Yahudun. Amma bisa dukkan alamu, Sharon ba ya bukatar shiga tsakanin Amirka kuma a harkkokin yankin a wannan lokacin. Sabili da haka ne dai ya fi gwammacewa, ya shiga tattaunawa kai tsaye da Falasdinawan.

A halin yanzu dai, ana kyautata zaton cewa, za a iya shawo kan wata matsala, game da batun sako fursunonin Falasdinawan da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila. bangarorin biyu, sun yarje kan kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakaninsu, wanda zai yi nazarin wannan batun. Amma tuni, Falasdinawan sun yi watsi da tayin da Isra’ilan ta yi musu na sako fursunoni dari 9 kawai, daga cikin fursunoni dubu 10an da ke hannunta.

A cikin yunkurin ganin an cim ma daidaito a taron kolin na Masar, ministan tsaron Isra’ila, ya bayyana cewa, dakarun kasar za su dakatad da farautar Falasdinawan da suke yi a yankunan da Isra’ilan ta mamaye. Bayan haka kuma, jami’an Isra’ilan sun ba da sanarwar cewa, dan jagoran boren nan na Intifada Marwan Barghouti, mai shekaru 19 da haihuwa, zai kasance daya daga cikin farkon Falasdinawan da Isra’ilan za ta sako daga kurkuku a cikin wannan makon.