1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar da Shugaban Burkina Faso Blaise Compaore ya kawo birnin Berlin.

Mohammad Nasiru AwalMarch 12, 2004

To shi dai shugaba Blaise Compaore ya kawo wannan ziyara ne bisa wata gayyata ta musamman daga shugaban tarayyar Jamus. Shugaban na Burkina Faso ya kwashe yini biyu yana rangadin fadar gwamnatin ta Jamus a cikin yanayin sanyin hunturu, kafin ya ziyarce zuwa biranen Potsdam da Bremen. Muhimman abubuwan da ya tattauna tare da shugaban Jamus Johannes Rau da ministan harkokin waje Joschka Fischer da ministar kula da ayyukan raya kasashe masu tasowa Heidemarie Wieckzorek-Zeul sun hada da batun huldar dangantaku tsakanin Jamus da Burkina Faso. A cikin wata hira da tashar DW ta yi da shi shugaba Blaise Compaore ya tabbatar da cewar a halin da ake ciki akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kasarsa da Jamus.

"Da farko dai wannan ziyara ta ba ni damar mika godiya ta ga tarayyar Jamus dangane da dinbim taimakon raya kasa da take ba Burkina Faso. Hadin kai tsakanin kasashen biyu na da karfi ainun, saboda haka muna rokon gwamnatin Jamus da ta ci-gaba da gudanar da ayyukan raya kasa a Burkina Faso."

A shekara ta 2003 da ta 2004 Jamus ta yiwa Burkina Faso alkwarin ba ta taimakon raya kasa na kudi Euro miliyan 36. Hakan dai na nuni ne da cewa Jamus na taimakawa irin muhimmiyar rawar da Burkina Faso din ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Afirka Ta Yamma. Wannan kasa dai memba ce a cikin jerin kungiyoyin yankuna dabam-dabam na Afirka dake ba da gagarumar gudummawa wajen yin sulhu tare da wanzar da zaman lafiya a yankunan da ake fama da rikice-rikice da yake-yaken basasa a Afirka.

Wani abin da aka tattauna a birnin Berlin yayin wannan ziyara ta shugaba Compaore, shine wani shirin daidaita cinikin auduga na kasashen duniya, wanda Burkina Faso tare da wasu kasashen Afirka 3, wato Benin, Mali da kuma Chadi ke ciki. Wannan shiri dai na yin kira da a rage ko kuma a sojke dinbim kudaden tallafi da ake ba manoman auduga a kasashe masu ci-gaban masana´antu kamar Amirka da kungiyar tarayyar Turai. Shugaba Compaore yayi kyakkyawan fatan cewa Jamus zata taimaka a kai ga wannan matsayi.

"Yana da muhimmanci ga samun ci-gaban mu idan muka samu shiga kasuwannin duniya. Domin idan ba´a bude mana kofofin kasuwannin ba, to da wuya zamu iya samun kudaden da muke bukata don gudanar da ayyukan raya kasa ga al´umomin mu."

Tun lokacin da aka fara wannan shiri gwamnatin tarayyar Jamus musamman ministar raya kasashe masu tasowa Heidemarie Wieczorek-Zeul ke taimakawa don a cimma manufar da aka sa