1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Abiy Ahmed zai kai ziyara a Somaliland

Abdoulrazak Garba Babani
February 26, 2025

Firaministan Habasha Abiy Ahmed zai kai ziyara a kasar Somaliya domin tattaunawa don samun masalha a kan sabannin da ke a tsakanin kasashen biyu.

Hoto: Prosperity Party -Ethiopia’s ruling party

A wani sabon  muhimmin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula da aka shafe watanni ana yi tsakanin kasashen biyu.Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da Abiy Ahmed sun gana a gefen taron kungiyar tarayyar Afirka a tsakiyar watan Fabrairu, inda suka tattauna matsalolin da ke tsakanin kasashen su. Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne, tun a  watan Janairun shekara ta 2024 bayan Addis Ababa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da yankin da ya balle na Somaliland, na ba da hayar kilomita 20 na gabar tekun Somaliland ga  Habasha.