Ziyarar firaministar Burtaniya a Jamus
July 20, 2016 Merkel ta ambata hakan ne a wani jawabi da ta yi tare da firaministan Burtaniya Theresa May lokacin da ta kai mata ziyara a Berlin, inda ta ke cewar tattaunawa kan ficewar Burtaniya din daga EU za ta yiwu ne kawai in har dukannin matakan yin hakan sun kammala.
Firaministan Burtaniya din a nata bangaren ta ce ta na son yin aiki kafa da kafa da Jamus da sauran kasashen Turai don ganin kasar ta fice kamar yadda al'ummarta ke so, amma suna son yin hakan ne cikin tsari.
Mrs. May ta kuma ce kuri'ar raba gardamar da 'yan Burtaniya suka kada ta barin EU ta aike da sako na cewar su na son ganin an sanya idanu kan kwararar bakin haure to amma kuma suna son a maida hankali kan sha'anin da ya danganci kasuwanci tsakanin kasar da takwarorinta na Turai.