1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kokarin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya

Mahmud Yaya Azare
September 14, 2021

Firaministan Isra'ila ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Sharm al-Sheikh, a ziyarar da ke zama irinta ta farko da wani firaiministan Isra'ila ke kai wa Masar cikin tsukin shekaru 10.

Ägypten Scharm el Scheich | Treffen Ministerpräsident Israel Bennett und Präsident al-Sisi
Hoto: EGYPTIAN PRESIDENCY/AFP

Ziyarar da ke zuwa 'yan kwanaki kafin cikar shekara guda da cimma yarjejeniyar Abraham data kai ga Isra'ila ta kulla huldar jakadanci da kasashen Larabawa hudu da ada basa ga maciji da ita, wato Hadaddiyar daular Larabawa da Bahraini da Sudan da Maroko, wadanda suka bi sawun kasashen Masar da Jodan da ke da tsohuwar huldar jakadancin da Isra'ila tun a shekarar 1973.

Wannan ziyarar, kamar yadda shugaban Masar Abdulfattah al-Sisi ke tabbatarwa, yunkuri ne na kara tabbatar da zaman lafiya a yankin ta hanyar tattaunawa da kulla hulda, wanda aka gwada aka gani cewa, shi ne kadai ke haifar da makoma mai kyau a alakar da ke tsakanin kasashen yankin.

Hoto: Nidal Eshtayeh/XinHua/picture alliance

"Masar ta jima tana fada wa Isra'ila cewa, tattaunawar zaman lafiya da Falasdinawa don cimma kafuwar kasarsu shi ne zaman lafiyarta da zaman lafiyar yankinmu. Shi ya sa a yanzu muka tattauna batun tabbatar da aiki da tsagaita wuta a fadin yankin, da kuma hanyoyin da za,a bi wajen sake gina Gaza da farfadado da tattalin arzikinta."

A nasa bangaren firaministan Isra'ila Naftali Bennett, wanda ke zama firaiministan isra'ila na farko da ke kai ziyara Masar cikin tsukin shekaru goma, ya yi fatan Kairo zata taimaka wajen shawo kan Falalsdinawan don cimma zaman lafiya mai dorewa a yanki.

"Mun tattauna batutuwan da suka shafi alakarmu ta tsaro data kasuwanci da Masar a hannu guda, kamar yadda muka fahimci juna kan mahimmancin yin aiki tare don sake gina Gaza da sasantawa da Falalsdinawa."

Hoto: Sebastian Scheiner, Pool/AP/picture alliance

Duk da kyakkyawan tasirin da ake ganin wannan ziyara da shi wajen yiwuwar farfado da tattaunawar zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya, sai dai masharhanta irin su Taufeeq Abul-ula na ganin cewa, ba a kama hanyar da zata bulle ba.

"Mu sanya hakkokin Falalsdinawa na kafuwar kasarsu da ake son yi, ta hanyar maye gurbin hakan da basu 'yan kudaden da za su sake gina garuruwansu da kyautata tattalin arzikinsu, wannan tamkar an yi kitso da kwarkwata ne, domin zai jawo lafawar lamura ne na dan lokaci kafin daga baya su sake dagulewa."