1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Jonathan a Borno da Yobe na shan suka

March 6, 2013

Shugaba Jonathan na Najeriya na shirin kai ziyara a Borno da Yobe domin shaidar da barnar da rikicin Kungiyar Boko haram ya haifar. Sai dai kungiyo sun yi kira da a juya ma sa baya saboda rashin kulawa da su da ya yi.

Titel: DW_Nigeria_Integration2 Schlagworte: Nigeria, Präsident, Goodluck Jonathan Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 04. April 2011 Aufnahmeort: Abuja, Nigeria Bildbeschreibung: Präsident Goodluck Jonathan
DW_Nigeria_Integration2Hoto: Katrin Gänsler

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban na Tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan zai ziyarci wadannan yankunan tun lokacin da hare-hare suka kazanta sama da shekara uku da suka shude. Al'ummar wannan yaki na ganin cewa shugaban da ma daukacin mukarraban ba na nuna halin ko oho wata kila don jam'iyyun adawa ne mulki a jihohin na Borno da Yobe. Tun a makon da ya wuce ne gwamnonin adawa suka zaga garin har ma shiga kasuwa duk da barazanar da ake musu na gamuwa da tashin Bama-Bamai. Haka kuma gwamnonin adawan sun ba da gudumowar Naira Miliyan 200 ga jihohin da abin ya shafa.

Hare-haren Borno da Yobe sun lamshe rayuka da dukiyoyiHoto: picture-alliance/dpa

Matsayin kungiyoyi game da ziyarar Jonthan

Kungiyoyin da ke kare muradun arewacin Najeriya sun shafe kwanki biyu suna nazari a birnin kaduna tare da fitar da matsayinsu game da wannan ziyara ta Jonthan a borno da Yobe. Jagoran wanan gamayyar da ake yi wa lakabi da Citizens Arewa for Change, Ashir Sheriff ya danganta ziyarar da "yaudara daga Jonathan saboda shekaru hudu aka shafe ana cin zarafin mutane, ana kwace dukiyoyinsu ba tare da ya nuna tausayawa ga mutanen Maiduguri da kuma Damaturu ba."

Illolin hare hare a Arewacin Najeriya

Wasu mazauna yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya sun nunar da cewa shugaban kasa ya yi fargar daji saboda ziyarar ta sa ba za ta amfani komai ba. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu sakamkon hare hare da aka kai a wadannan jihohi guda biyu. kana kungoyin taimakon raya kasa sun fice daga yankin na arewa i zuwa kudancin kasar. A daya hannun kuwa tattalin arzikin yankin ya durkushe. Saboda haka ne Ashir Sherif ya yi "Kira ga 'yan Borno da mutanen Yobe da ka da su fito su yi wa Jonthan maraba. Jami'an gwamnati ne ya kamata sun tare shi domin su baiyana ma sa irin laifin da ya yi wa mutanen Maiduguri."

Ba yau Jonathan ya fara shan suka daga talakawa baHoto: dapd

Dukkanin jihohin da shugaban zai ziyar ta dai sun tsaurara matakan tsaro inda tuni aka rufe wasu hanyoyi da shugaban zai bi don tabbatar da cewa ya yi ziyayar ba tare da samun wani kalubale ba.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mouhamadou Awal