Ziyarar Merkel a China da Japan
August 23, 2007Shugabar gwamnatin jamus Angela na shirin fara rangandin aiki zuwa kasashen China da Japan,da fatan cewar wannan ziyara da zata kai zuwa manyan jagoran tattalin arziki na yankin na Asia ,zai taimakawa kokarinda takeyi na daukar sawun gaba wajen yakar matsalar dumamar yanayi da duniya ke fuskanta.
Ayayin wannan ziyara da zata fara raanar lahadi wanda kuma ke zama irinsa na farko a kasar ta Japan,tun da ta haye karagar mulki a watan nuwamban 2005,Merkel zata gabatar da jawabi na musamman adangane da cikan shekaru 10 da rattaba hannu a yarnjejeniyar nan ta kyoto,adangane da matsalar sauyin yanayi.
Bugu da kari wannan ziyara tata zuwa kasashen biyu dake tafiyar da harkokin kasuwanci da Jasmus a yankin,yazo ne adaidai lokacin da tattalin arzikin China ke cigaba da bunkasa da yaduwa a duniya,ayayinda ita kuwa japan take samun ingantuwan tattalin arziki.