Ziyarar Merkel a kasar Daular Larabawa
May 24, 2010Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa kasar hadaddiyar daular larabawa domin fara ziyarar aiki na kwanki hudu a zagaye na biyu na rangadin da ta kai yankin a matsayin shugabar gwamnati. Mataimakin shugaban kasar Sheikh Mohammed bin Said al-Nahyan shine ya tarbi shugabar gwamnatin da yan tawagarta a lokacin da suka isa kasar. A ranar Talata kuma shugabar gwamnatin za ta kai ziyara birnin Masdar. A jadawalin ziyarar za ta sanya hannu akan wata yarjejeniyar aikin man fetur na tsabar kudi euro miliyan dubu daya wadda zaá kulla tsakanin kasar ta daular larabawa da wani kamfanin Jamus. A yayin wannan ziyara ta yankin Gulf shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta kuma ziyarci kasashen Bahrain da Qatar da kuma Saudiyya. Yankin na Gulf dai ya kasance yanki mafi bunkasar cigaban tattalin arziki a duniya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko BalaEdita : Yahouza Sadissou Madobi