1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel ga sojojin Jamus a Afganistan

Mohammad AwalMarch 12, 2012

Shugabar gwamnatin ta Jamus wadda ziyararta ta zo kwana guda bayan kashe fararen hula da wani sajon Amirka yayi, ta yi wa shugaba Hamid Karzai jaje.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) steht am Montag (12.03.12) in Masar-i-Scharif (Afghanistan) waehrend ihres Kurzbesuches mit dem Generalinspekteur der Bundeswehr, Volker Wieker (l.), und dem Kommandeur RC North, Erich Pfeffer (r.), am Ehrenhain, der Gedenkstaette fuer die im Einsatz der Internationalen Sicherheitsunterstuetzungstruppe (ISAF) in Afghanistan gefallenen deutschen Soldaten. Merkels Besuch bei den deutschen Soldaten in Afghanistan soll nur einen Tag dauern und war seit laengerem geplant, teilte das Bundespresseamt mit. Ein Flug nach Kundus sei wegen schlechten Wetters nicht moeglich. Merkel hatte zuletzt am 18. Dezember 2010 Afghanistan besucht. Zuvor war sie 2007 und 2009 in dem Land. (zu dapd-Text) Foto: Kristina Dunz/Pool/dapd
Shugabar Gwamnatin Jamus Merkel a Masar-i-SharifHoto: dapd

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna shakku ko dakarun ƙungiyar NATO za su iya ficewa daga Afganistan a shekarar 2014 kamar yadda aka tsara. A wata ziyarar ba zata da ta kaiwa sojojin Jamus a sansaninsu dake yankin Mazar-i-Sharif Merkel ta ce ko da yake an samu ci-gaba a ƙoƙarin yin sulhu da 'yan Taliban, amma hakan ba kai matsayin da za a iya janye dakarun ba. Da sanyin safiyar wannan Litinin Mekel ta isa yankin a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, domin gane wa idonta aikin da sojojin Jamus ke yi a Afganistan. Daga nan ta buga wa shugaban Aganistan Hamid karzai waya don yi masa jaje game da aika-aikar da sojan Amirka yayi a kudancin ƙasar.

"Daga nan Mazar-i-Sharif na yi magana da shugaba Karzai inda na sake jaddada masa jaje na game da mummunan aikin da sojan Amirka yayi a ranar Lahadi."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe