1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100112 China Iran

Zainab MohammedJanuary 10, 2012

Rikici kan Nukiliya tsakanin ƙasasahen yammaci na Turai da Iran dai sai ƙara tsanata ya ke yi a kowace rana

epa03054714 (FILE) A file photograph showing US Treasury Secretary Timothy Geithner (R) and White House Budget Director Jack Lew (L) take questions from members of the news media during a news briefing at the White House in Washington DC, USA, 19 September 2011. Media reports om 09 January 2012 that William Daley is stepping down as White House chief of staff and budget director Jack Lew is taking over President Obama's team as it heads into an election year. EPA/MICHAEL REYNOLDS *** Local Caption *** 00000402925654 +++(c) dpa - Bildfunk+++Timothy Franz Geithner [gaɪtnər] (* 18. August 1961 in Brooklyn, New York City) ist der 75. Finanzminister der Vereinigten Staaten (United States Secretary of the Treasury). Am 26. Januar 2009 wurde seine zuvor erfolgte Ernennung durch US-Präsident Barack Obama vom US-Senat bestätigt.
Timothy GeithnerHoto: picture-alliance/dpa

A ƙarshen mako ne dai Tehran ta ƙara sanar da  shirinta na inganta sinadran Uranium a tasharta da ke Fordo, batu daya janyo martanin gargaɗi da babbar murya daga ɓangaren Amurka. Tuni dai Amurkan ta shirya sabbin takunkumi akan Iran, a daidai lokacin da ministan harkokin kuɗi Timothy Geithner ke ziyarar kwanaki biyu a ƙasar China.

China dai ta kasance ƙasa da ta fi kowace sayen Mai daga Iran, dan gane da haka ne take jan kafa a dangane da amincewa kowane mataki da ake neman dauka akan harkokin man Tehran. China na da bukatun na Makamashi mai yawan gaske, sakamakon bunkasar harkokin kasuwancinta, wanda kuma take dogaro kacokan kan Iran. Wajen kashi 11 na yawan man da China ke saye dai daga Iran yake fitowa, wanda yakai wajen kimanin Ganga dubu 560 a kowace rana. Bayan Saudi Arabia da Angola dai, Iran ce kasa ta uku dake samarwa China Mai. Dangane da hakane kaifin martanin Beijing wa Amurka yake da muhimmanci, kan kokarinta na taɓa babban Bankin Iran wadda ke tafiyar da lamuran mai..

Acewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Liu Weimin  " ɗaukar matakan kakabawa Iran takunmi ba shine kadai zai warware wannan rikici na shirin Nukiliyarta ba".  Ya kara da cewar babu matakan da zasu fi tattaunawa da tuntubar juna yin tasiri. Daura da haka babu yadda za'ayi dokokin cikin gida suyi tasiri akan na kasa da kasa. Babu dalilan yin hakan.

Hoto: picture-alliance/dpa

Ziyarar ta ministan harkokin kuɗin  Amur ka Timothy Geithner a Beijing dai nada nufin tattauna matsalolin tattalin arziki da Duniya take fama dasu, da kuma karuwar damuwa dangane da shirin Nukiliyar Iran. Kazalika agendar tattaunawar zata kunshi matakan matsin lamba akan babban bankin Iran, wanda shine ke lura da dukkan kuɗaɗen shigara da kasar ke samu daga albarkatun Mai da ake fitarwa waje. A talatar nan ce Geithner ya gana da mataimakin shugaban ƙasa Wang Qishan, yayinda zai gana da shugaba Wen Jiabao da jami'an harkokin kudi na Chinan a ranar laraba.

China dai bata yi imanin cewar harkokin nukiliyar Iran nada babbar barazana kamar yadda Amurka da ƙasashen yammaci ke nunarwa ba, sai dai akwai bukatar magabatan Tehran su dada fitowa fili wajen nunarwa Duniya cewar, ba da wata muguwar manufa suke inganta sinadaran Atom ba, sai dai kawai domin wadata al'ummar ƙasar da makamashi mai inganci.

Tashar makamashin IranHoto: Fars

Li Guofu ƙwararre ne kan Iran a cibiyar nazarin lamuran ƙasa da ƙasa dake birnin Beijing, wanda ya ce  " matsayin China a bayyana yake, muna adawa da shirin kera makamin Nukiliya a ɓangaren Iran, amma a matsayinta na membar hukumar kula da makamashi ta ƙasa da ƙasa kuma wadda ta sanya hannu akan yarjejeniyar haramta yaɗuwar makaman nukiliya, Iran ta na da 'yancin samarwa da ƙasar ta ingantaccen makamashi na Nukiliya. Duk da cewar rahotan hukumar IAEA na bayan nan na zarginta da kera makamai, babu wata shaida a rahotan dake tabbatar da hakan". 

To sai dai sakamakon wannan yanayi da ake ciki, kasar ta China na takatsantsan dangane da harkokin kasuwancinta ta Iran. Rahotannin kafofin yada labarun ƙasar ta China na nuni da cewar, kampanonin mai na Beijing sun fara rage zuba jari a Iran, kazalika an rage yawan man da ake shigowa dashi data Tehran ɗin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita          : Mohammad Nasir Awal