1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jaddada goyon baya ga Ukraine

June 16, 2022

Shugabannin Jamus da Faransa da Italiya sun ziyarci birnin Kyiv na Ukraine, a wani mataki na nuna goyon bayansu yayin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a gabashin kasar ta Ukraine.

Olaf Scholz I  Emmanuel Macron I Mario Draghi I Klaus Iohannis und Volodymyr Zelenskiy
Hoto: Ludovic Marin/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf scholz da Emmanuel Macron na Faransa da da kuma Firanministan Italiya Mario Draghi sun kai ziyara birnin Kyiv don ganewa idanunsu mummunan ta'asar da Rasha ta aikata a Ukraine. Wannan dai shi ne karon farko da shugabannin uku na kasashen kungiyar tarayyar Turai suka kai ziyara birnin na Kyiv tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine  din a ranar 24 ga watan Fabarairun 2022

Shugabannin sun fara yada zango ne a birnin Irpin da ke wajen birnin Kyiv, inda aka zargi dakarun Rasha da aikata mumunan ta'asa tun farkon fara yaki a tsakanin kasashen biyu.

Yayin da yake jawabi, shugaban gwamnatin Jamus Olaf scholz ya yi tir da mummunan ta'adin da ya ce Rasha ta tafka.


"Babban tashin hankali ne wannan yakin ke haifarwa, abun da muka gane wa idanunmu ya fi abun da muke tsammani muni. Yaki ya rutsa da fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba, an lalata gidaje da ma birnin bakin daya. Duk da cewa babu wasu gine-gine na soji, amma hakan ya bayyana kararar irin rashin tausayi na Rasha wanda burinta shi ne ta cimma mumumman manufarta. Ya kamata mu sanya hakan a kawunanmu a duk wani hukunci da za mu yanke."

A nasa bangaren shugaba Emmanuel Macron ya ce za su ci gaba da mara wa Ukraine baya babu gudu babu ja da baya, har sai sun ga abun da ya ture wa buzu nadi.

Gwamnatin Kyiv dai na rokon sauran kawayenta na yammacin Tura da su kara tallafa mata da karin makamai. Ko da yake a baya-bayan nan Amirka ta sanar da sake aike wa Ukraine karin tallafin kusan dala biliyan daya  na kayan soji, wannan dai shi ne kaso mafi girma na tallafin makamai da kayan aiki tun da aka fara yakin Ukraine.

To sai dai ga Dmitry Peskov kakakin shugaba Vladmir Putin na Rasha a martaninsa kan ziyarar shugabannin yammacin Turan, fadar Kremlin na fatan shugabannin da ke ziyarar za su bukaci shugaba Zelensky da ya dubi lamarin da idon basira ba kawai su mayar da hankali wajen tura wa Ukraine din karin makamai ba.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna