1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Paparoma a yankin Gabas ta Tsakiya

YahouzaSeptember 14, 2012

Paparoma Benedikt na 16 zai gana da hukumomin Lebanon da shugabannin addinai game da zaman lafiya a duniya.

epa03315036 (FILES) A file photo dated 16 June 2010 showing Papal butler Paolo Gabriele (left, front) travelling with Pope Benedict XVI in the Vatican. Gabriele was released to house arrest last weekend after spending 60 days in detention. Vatican officials say he would most probably face trial on charges of stealing and leaking to Italian journalists letters and papers from the Pope's apartments. His trial is likely to start in the Autumn EPA/ETTORE FERRARI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan Juma'ar ne Paparoma Benedikt na 16 ya fara yin wata ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya inda ya fara yada zango a kasar Lebonon. Wannan ziyarar ta kwanaki ukku za ta bashi damar isar da sakon zaman lafiya a kasar Siriya inda ake ci-gaba da gobza fada wanda kuma bisa ga dukkan alamu ke shirin daukar wani sabon salo na rikicin addini. Rahotani daga fadar Vatican sun ce da saukar sa a filin jirgin saman Beyrouth na Lebonon Paparoman dan shekaru 83 zai fara ganawa da hukumomin kasar musamman Michel Sleiman wanda shi ne daya tillo shugabn wata kasar yankin kasashen larabawa wanda ba musulmi ba. Wannan ziyarar ita ce karo na biyu a yankin na gabas ta tsakiya, bayan wani rangandin ya yayi a shekara ta 2009 a kasar Saudiya.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita : Yahouza Sadissou Madobi