1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Putin zuwa Turkiyya

December 3, 2012

A Litinin din nan ce ake sa ran isar Shugaba Vladimir Putin zai je Turkiyya don tattauna irin banbancin ra'ayin da ke akwai tsakanin Rasha da Turkiyya kan halin da ake ciki a Siriya.

Hoto: AFP/Getty Images

Yayin wannan tattaunawar rahotanni na nuna cewar Turkiyya za ta yi kokarin shawo kan Shugaba Putin da ya jaye irin goyon bayan da ya ke bawa Shugaba Assad wadda kasar sa ke cikin wani yanayi na yakin basasa biyo bayan rajin da 'yan adawa su ke yi na ganin ya sauka daga gadon mulki to sai dai ana ganin da wuya Rasha ta juyawa gwamnatin Assad baya.

Baya ga tattanawar da shugabanin kasashen biyu za su yi kan rikicn na Siriya, ana kuma ganin Shugaba Putin zai yi amfani da ziyarar ta sa domin nunawa duniya cewar ya na cike da koashin lafiya sabanin rade-radin da ake ta yi cewar ya na fama da jinya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas