1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Schröder A Aljeriya

October 18, 2004

Bayan kammala ziyararsa ta yini biyu ga kasar Libiya shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya ya da zango a Aljeriya akan hanyarsa ta dawowa gida inda suka gana ido hudu da shugaba Bouteflika a ranar asabar da ta wuce

A lokacin ganawar tasu sun yi musayar yawu akan batutuwan al’adu da rikicin Yankin Gabas ta tsakiya da ya ki ci ya ki cinyewa. Amma fa babban abin da aka fi mayar da hankali kansa a wannan ziyarar, wadda ita ce ta farko da wani shugaban gwamnatin jamus ya kai Aljeriya tun misalin shekaru 30 da suka wuce shi ne, maganar kudi da kuma ta ta’addanci. A lokacin da yake bayani game da haka shugaban gwamnati Gerhard schröder cewa yayi:

Dukkanmu biyu mun hakikance cewar matakan soja da ‚yan sanda kawai ba zai wadatar ba, wajibi ne a ba da cikakken la’akari da matsaloli na rayuwa da zamantakewar jama’a a kasashen da lamarin ya shafa. Akwai bukatar kirkiro wata kyakkyawar manufa ta kyautata makomar rayuwar mutanen da ba su da wuyan karkata zuwa ga tsattsauran ra’ayi na tsageranci da ga-ni-kashe-ni.

An dade ana fama da gibi a game da wannan manufa, inda aka yi shekara da shekaru dakarun musulmi masu tsananin kishin addini da sojan kasar Aljeriya ba sa ga maciji da juna. Dukkan bangarorin biyu sun yi amfani da matakai na rashin imani a neman karya alkadarin juna. Amma ga alamu a yanzun wannan yayi ya gushe. Domin kuwa tun bayan tsautsayin nan na 11 ga watan satumban shekara ta 2001 Aljeriya ke samun goyan baya musamman daga Amurka domin murkushe masu zazzafan ra’ayin kishin addini ba ji ba gani.

Ita dai Aljeriya, wacce ta kyautata alakarta da kasashen Amurka da Spain da kuma Faransa, ta dade tana mai bin tafarkin gurguzu, kuma a saboda haka take fama da tafiyar hawainiya a kokarinta na komawa karkashin tsarin demokradiyya da sakarwa da harkokin kasuwanci mara. Kasar na bukatar hadin kai daga Jamus domin sabunta hanyoyinta na sadarwa. A halin yanzu haka akwai kamfanoni da dama na kasar dake gudanar da ayyukansu a Aljeriya, kuma wannan kwangila a daya bangaren tana taimakawa wajen kare makomar guraben ayyukan yi a nan cikin gida. To sai dai kuma ba kasafai ba ne ba, injiniyoyi da sauran kwararrun ma’aikata na Jamus ke sha’awar gudanar da ayyukansu a Aljeriya saboda matsaloli na tsaro. Amma fa ba shakka da zarar al’amura sun dada daidaituwa za a samu karin kwararrun ma’aikatan da zasu amince da gudanar da ayyukansu a kasar ta arewacin Afurka.