1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300511 Zuma AU Libyen

May 30, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sake aika wata tawaga zuwa Libiya domin ci-gaba da yunƙurin shawo kan rikicin ƙasar a siyasance.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta KuduHoto: picture-alliance/dpa

A daidai lokacin da shugaban ƙungiyar ƙawance ta NATO Anders Fogh Rasmussen ke iƙirarin cewa mulkin shugaba Mu'ammar Gaddafi na gab da ƙarewa, Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sake aikawa da wata tawaga zuwa Libiya a ƙarƙashin jagorancin shugaban Afurka ta Kudu Jacob Zuma domin shawo kan rikicin siyasance, kuma a wannan karon, da alamun cewa ziyarar zata buɗe hanyar samar da irin sassantawar da ƙasar ke bukata.

Frime Ministan Libiya Baghdadi al-Mahmudi ne ya tari shugaba Jacob Zuma a filin jirgin sama, sa'oi kaɗan bayan da kafofin yaɗa labaran ƙasar suka bada sanarwar cewa dakarun ƙungiyar ƙawance ta NATO sun yi luguden wuta a garin Zilten da ke yamma da birnin Misurata wanda kuma ya yi sanadiyyar hallakar mutane 11.

Ofishin shugaban na Afurka ta Kudu, ya ce Zuma, yana neman a tsagaita wuta a ƙasar Libiyan, domin a inganta ayyukan agaji a kuma kawo irin sauye-sauyen da zasu daƙile mafarin wannan rikici wanda aka fara daga tsakiyar watan Fabrairu.

'Yan tawaye na samun ɗaurin gindin sojojin NATOHoto: dapd

Shi dai Mu'ammar Gaddafi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Tarayyar ta Afirka, kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fi zuba jari a Nahiyar Afirkan baki ɗaya, abokin tsohon shugaba Nelson Mandela ne, kuma yayi shekara da shekaru yana goyon bayan jamiyyar ANC wadda ke mulki a Afurka ta Kudun. Maite Nkoana-Mashabane ita ce ministan harkokin wajen Afirka ta Kudun kuma tayi ƙarin bayani dangane da ziyarar.

"Shugaba Jacob Zuma, ya je Libiya ne domin ya cigaba da yunƙurin aiwatar da ƙudurin Ƙungiyar Tarayyar Afurka na neman samar da yarjejeniyar sulhu a siyasance"

Ziyarar da tawagar ta kai a karon farko, bata yi wani kataɓus ba saboda Gaddafi bai amince da miƙa mulki ba wadda ke zaman ɗaya daga cikin sharuɗɗan da 'yan tawayen suka bayar idan har ana neman a yi wata yarjejeniya.

A yanzu haka dai, Jiragen yaƙin NATO na cigaba da kai hare-hare ta sama a birnin Tripoli. A wani taron wakilan Majlisar ƙungiyar NATO, shugaban ƙungiyar Anders Fogh Rasmussen ya nunar da cewa matakin ƙuingiyar na gab da cin nasara wajen fidda Gaddafi daga kujerar mulkin ƙasar inda ya nuna cewa muƙarraban sa na gida da na waje na cigaba da keɓe sa, kuma mafi yawancin waɗanda ke gwamnatin na sa suna barin ƙasar ko kuma canza sheƙa.

Shugaba Mu'ammar Gaddafi ya dage cewa ba zai sauka baHoto: dapd

A yankin Gabashin Libiyan Mustapha Abdul Jalil, wanda ke jagorantar gwamnatin riƙon ƙwaryar yankin ya yi farin cikin da kiran da ƙungiyar ƙasashe masu manyan masana'antu na G8 suka yi na Gaddafi ya sauka, to sai dai a na ta martanin, gwamnatin Libiya ta ce duk wani shiri na kawo sulhu a rikicin, dole ne ya bi ta hanun ƙungiyar Tarayyar Afirka saboda ƙungiyar G8 bata da hurumin ɗaukar wani mataki dangane da batun kamar yadda itama ministar harkokin wajen Afurkan ta Kudu ta bayyana.

"Wannan ziyara ce ta biyu amma a wannan karon tawagar ta fi bada muhimmanci ne ga taswirar hanyar ƙungiyar wadda ta nunar da cewa matsalar Libiya ta siyasa ce, saboda haka, ƙungiyar bata amince da cewa amfani da ƙarfin soja zata iya shawo kan matsalar Libiyan ba."

'Yan tawayen ƙasar dai na nan kan bakan su, na cewa ba zasu amince da wata yarjejeniyar sulhu da bata tanadi shugaba Mu'ammar Gaddafi ya sauka daga kujerar mulkin Libiyan ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal