1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAngola

Angola: Shugaba Joe Biden na ziyarar aiki

December 2, 2024

Shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya kai ziyara kasar Angola, domin cika alkawarin da ya yi na kyautata alaka da nahiyar Afirka.

Amurka | Joe Biden | Ziyara | Angola | Cape Verde
Joe Biden a Cape Verde kafin ya karasa AngolaHoto: Ben Curtis/dpa/picture alliance

Ziyarar na zuwa ne makonni kalilan kafin ya sauka daga karagar mulki a watan Janairu, inda Joe Biden ke zaman shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara kasar ta kudancin Afirka mai arzikin mai tun bayan da ta sami 'ancin kai daga kasar Portgula a shekarar 1975. A Luanda babban birnin kasar Shugaba Biden da ya karbi ragamar mulki a watan Janairun 2021, zai gudanar da ayyuka da suka hada da sanya hannu kan yarjeniyoyi na siyasa da tsaro da kuma kulla huldar tattalin arziki tsakanin Amurka da Angolan. An dai shirya sanya hannu kan wasu muhimman ayyukan tattalin arziki, wadanda ke da muhimmanci ga bangarorin biyu. Akwai muhimman harkokin tattalin arziki da aka samar a Angola da tallafin Amurka, wadanda ake amfani da su a yanzu da kuma ake fatan ginawa a nan gaba kamar gina matatar mai a arewacin kasar. To amma babban aikin shi ne gina da'irar hanyar da aka yi wa lakabi da "Lobito Corridor" da ta hada da gina layin dogo, wanda zai hada Lobito da ke bangaren Angola na Tekun Atlantika da yankin Zambiya mai arzikin tagulla ya dangana da wani sashe na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo mai arzikin Cobalt sannan ya hade yankunan tsakiyar Afirka masu arzikin ma'adanai da tashar jiragen ruwa a Tekun Atlantika.

Hoto: Yuri Gripas/ABACAPRESS/picture alliance

Manufar ita ce gina layin dogo mai tsawon kilomita 550 a Zambiya da kuma titin mota mai tsawon kilomita 260 da tallafin Amurka da kungiyar Tarayyar Turai da Bankin Raya Kasashen Afirka da zai bayar da gudunmawar dala miliyan 500 a aikin da zai ci dala miliyan 1000 da miliyan 600, a cewar Claudio Silva masanin siyasa a kasar Angola. Shugaban Angola dai yana so ya yi hulda da manyan kasashe masu tattalin arziki, domin amfana daga gogayyar da za su yi da juna. Rasha ita ma tana da nata muradin, ko da yake Angola ta san matsayinta da muhimmancinta a yankin. Ba abu ne mai sauki ba yadda za ta tafiyar da lamura a mu'amalarta da abokan huldar. Wani abin la'akari shi ne a baya-bayan nan dangantaka ta fanni soja tsakanin Amurka da Angola ta kara karfi, inda masana ke hasashen Amurka na so ta kafa sansanin sojojinta a arewacin kasar. A waje guda dai ziyarar Shugaba Biden a Angola babu shakka ziyara ce mai dimbin tarihi, sai dai kuma ziyarar ba za ta sauya komai ba nan take a cewar Kinkinamo Tuassamba kwararren masanin siyasar kasa da kasa. Ya ce 'yan bokon Angola yan kalilai ne mai yiwuwa za su ci moriyar zuba hannun jarin na Amurka, kamar yadda ya kasance da manyan ayyukan da Chaina ta aiwatar a kasar. Matasan Angola wadanda su ne mafi rinjaye a cikin al'ummar kasar, na fama da tsananin rashin aiki da zaman kashe wando.