Ziyarar shugaban bankin duniya a nahiyar Afrika
July 12, 2006Shugaban bankin duniya Paul Wolfowitz na ziyarar gani da ido a nahiyar Afrika gabanin taron shugabanin kasashe masu cigaban masanaántu na duniya G8.
Shugaban na Bankin duniya Paul Wolfowitz wanda ya fara yada zango a kasar Habasha, ya ci alwashin cewa wajibi ne manyan kasashe masu arziki su cika alkawuran da suka yi a bara na taimakawa ta hanyar samar da kyakyawan yanayi ga kasashe matalauta na Afrika domin fitar da ita daga kangin talauci tare kuma da habaka cigaban alúmomin nahiyar.
A ranar Talata shugaban na Bankin duniya ya ziyarci makarantu a arewacin lardin Amhara a kasar Habasha daya daga cikin yankunan da kasashen masu arziki na duniya suka yi alkawarin samar da gudunmawar jin kai domin ciyar da alúmomin gaba.
Bankin na duniya ya amince da bada cikakkiyar kariya ga wasu ayyuka na muhimman bukatun rayuwa a wannan shekarar yayin da kasashen masu bada gudunmawar jin kai suka yi alkawarin cigaba da ayyukan da suke gudanarwa a kasar Habasha bayan dakatar da tallafin da suke bayarwa kai tsaye saboda dirar mikiya da gwamnatin ta yiwa kungiyoyin adawa a kasar gabanin zabe.
Shirin tallafin dai ya kunshi gudunmawar agaji ga kananan hukumomi domin samar abubuwan bukatun rayuwa kamar ruwan sha, harkokin lafiya dana ilimi da kuma gina hanyoyi.
Wannan ziyarar dai ita ce ta biyu da shugaban Bankin na duniya ya kai zuwa nahiyar Afrika tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin bankin a shekarar data gabata. Bankin dake zama babban mai bada rance ga kasashen Afrika. A karshen mako shugaban na Bankin duniya zai katse ziyarar da yake yi a kasashe bakwai na Afrika domin halartar taron shugabnin kungiyar G8 da zai gudana a birnin St Petersburg a kasar Rasha.
A wannan taron ne kuma yake fatan yin matashiya ga shugabanin na duniya a game da alkawuran da suka yi a bara na rubanya gudunmawa jin kai ga kasashen Afrika da daidaita harkokin cinikayya a tsakanin su da kuma yafewa kasashen Afrika bashin da suke bin su.
A yayin ziyara da shugaban bankin duniyar Paul Wolfowitz ya kai ga makarantu a kasar ta Habasha, malamai da dama sun koka a game da karancin kayayyakin koyarwa musamman litattafai da kuma cunkoson yara a ajujuwa. Wolfowitz ya yi alkawarin samarwa malaman kayayyakin kimiya da kuma littafai.
A kuma lokacin da ya ziyarci wani dakin shan magani ya lura mata da yayayen su, sun yi layi inda suke jiran karbar maganin ciwon malaria na zazzabin cizon sauro, wasu mutanen kuma na fama ne da cuttukan da suka shafi toshewar numfashi da sauran cuttukan da ake shaka ta hanyar numfashi, sai dai kuma kamar yadda ya lura, jamián nurse nurse ne kawai a asibitin amma babu likitoci.
A waje guda kuma shugaban na Bankin duniya ya yada zango a wata gona inda ya gwada noma da garmar shanu, cikin raha a zantawar da ya yi manoman yana cewa kai ina zato dai zan cigaba ne da aikin da na saba yi na yau da kullum.
Ya kuma shaidawa wasu jamian karamar hukuma dake lardin cewa Bankin duniya a shirye yake ya yi aiki tare da alúmomin domin taimaka musu ta fannin ilimi da lafiya, yana mai cewa a yayin da aka sami zaman lafiya da kwanciyar tare da tafarki na dimokradiya wannan kasa ta Habasha zata habaka.
Bugu da kari ya nemi jin ta bakin alúmomin kan yadda ake tafiyar da kasafin kudi da ake warewa da kuma shin ko suna tasiri a game da yadda ake kashe kudaden.
Daga bisani an yiwa Wolfowitz bayanai a game da wani shiri da Bankin duniyar zai gudanar a kogin Tana kogi mafi girma a kasar Habasha wanda ake fatan bunkasa masanaántu masu sarrafa kayan amfanin gona da kyautata wuraren shakatawa dana kamun kifi da kuma tashar samar da hasken wutar lantarki. A ranar Alhamis Shugaban na Bankin duniya Paul Wolfowitz zai ziyarci kasar Tanzaniya kafin ya wuce domin halartar taron kungiyar G8 a kasar Rasha.