1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban China Jintao a Amirka

Tijani LawalJanuary 20, 2011

Ƙasar Amirka ta yi wa shugaba Hu Jintao na China marhabin ta sha tara ta arziƙi ko da yake hakan ba ya nufin kawar da banbance-banbancen dake tsakanin ƙasashen biyu.

Obama da uwargidansa Michelle na yi wa shugaba Hu Jintao marhabin a fadar mulki ta White HouseHoto: AP

Barak Obama dai ya cika alƙawari, inda tun da farkon fari ya bayyanar cewar ba zai cika baki dangane da ziyarar shugaban ƙasar Chinar ba. Ba tare da wata rufa-rufa ba, shugaban Amirkan ya soki lamirin manufofin tsayar da darajar takardun kuɗin China:

"Na faɗa wa shugaba Hu cewar muna madalla da kasancewar ta ɗan ɗaga darajar takardun kuɗinta domin tayi daidai da kasuwar musayar kuɗaɗe. To sai dai kuma wajibi ne in sake nanata cewar har yau dai da sauran rina a kaba. Tilas ne a ƙara ɗaga darajar takardun kuɗin na Yuan daidai da mizanin musayar takardun kuɗi. Ta haka ƙasar zata samu kafar kyautata al'amuran cinikinta na cikin gida da dakatar da hauhawar farashin kaya."

Dangane da maganar girmama haƙƙin ɗan-Adam ma dai shugaban na Amurka mai lambar girmamawa ta zaman lafiya bai yi wata rufa-rufa game da ita ba:

Shugaba Barack Obama da takwaransa Hu Jintao bayan liyafar marhabin a fadar mulki ta White HouseHoto: AP

"Ina mai ƙara jaddada cewar wajibi ne akan Amirka ta tabbatar da dukkannin haƙƙoƙin ɗan-Adam na ƙasa da ƙasa, abin da ya haɗa har da 'yancin 'yan jarida da ikon faɗin albarkacin baki da zanga-zanga da kuma 'yancin addini. Shi kansa kundin tsarin mulkin ƙasar China ya tanadi waɗannan manufofi. Muna tattare imanin cewar, dukkan ƙasashe, abin da ya haɗa har da China, zasu fi samun nasara da yalwa ne idan suka kare waɗannan manufofi."

A nasa ɓangaren shugaba Hu Jintao ya taɓo maganar girmama haƙƙin ɗan Adam ɗin lokacin taron haɗin gtuiwa da manema labarai da shugabannin biyu suka gudanar. Kuma ko da yake har yau ƙasar ta China na ci gaba da tsare Liu Xiaobo mai lambar yabo ta zaman lafiya, a gidan kaso, amma shugaban cewa yayi:

Obama da Hu na taron haɗin guiwa da manema labarai bayan ganawarsuHoto: AP

"Girmama da kuma kare haƙƙin ɗan-Adam alhaki ne da ya rataya a wuyan ƙasar China kuma ta samu gagarumin ci-gaba akan wannan manufa."

To ko da yake dai maganar ta haƙƙin ɗan-Adam tana da muhimmanci, amma fa manufar tattalin arziƙi, ita ce aka fi mayar da hankali kanta a ziyarar ta Hu Jintao. Dalili kuwa shi ne tattalin arziƙi shi ne ainihin ginshiƙin dangantakar Chinar da Amirka. Domin kuwa a baya ga ƙasashen Kanada da Mexiko, China ce abokiyar murmin ciniki a'ala ga Amirka. Rahotannin masu nasaba da gwamnatin Amirka sun ce kimanin guraben ayyuka rabin miliyan a ƙasar sun ta'allaƙa ne akan kayan da take fitarwa zuwa China. A kuma lokaci guda Chinar na bin Amirka bashin da ya kai na dala miliyan dubu ɗari takwas. A sakamakon haka maganar kasuwanci ta fi ɗaukar hankali a shawarwari na bayan fage, inda aka kuma cimma yarjeniyoyi a ɓangarori da dama tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafi: Christina Bergman/Ahmad tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu