1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a Afirka Ta Kudu.

Mohammad Nasiru AwalJanuary 23, 2004
A tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da takwaransa na ATK Thabo Mbeki, dukkan su sun nuna gamsuwa da batutuwan da suka zanta a kai. To sai dai an jiyo mista Schröder na cewa ba su cimma matsaya daya game da kasar Zimbabwe ba, wadda har yanzu ATK ta ki fitowa fili ta kalubalanci gwamnatin shugaba Robert Mugabe. A game da huldar dangantaku tsakanin Jamus da ATK kuwa shugaba Thabo Mbeki ya yi nuni da cewa har yanzu akwai kyakkyawar hulda musamman ta tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. To amma duk da haka da akwai bukatar fadada wannan hulda. A halin da ake ciki Jamus ce ke matsayi na biyu a jerin kasashen da suka fi tafiyar da huldar kasuwanci da zuba jari a ATK. Da yake wannan hulda na da kyau, shugabannin biyu sun yi amfani da wannan dama wajen tabo batun wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara ta 2010, inda aka jiyo shugaba Mbeki na cewa mista Schröder na goyon bayan a ba ATK damar karbar bakoncin wasannin. Shi ma a nasa bangaren mista Schröder cewa yayi ko da yake bai kai wannan ziyara don tattauna batun wasannin cin kofin kwallon kafar ba, amma ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen gudanar da wadannan wasannin a ATK a shekara ta 2010.

Ko shakka babu shugaban gwamnatin Jamus na matukar kyaunar ATK da shugabanta Thabo Mbeki. Mista Schröder ya yaba da mulkin shugaba Mbeki musamman dangane da tabbatar da dorewar mulkin demukiradiyya da ´yanci ga kowa da kowa. A bana ne dai ATK ke bikin cika shekaru 10 da kawo karshen mulkin nuna wariya. Schröder ya kuma tabo batun tsaro da zaman lafiya, inda ya ba da misali da ATK da cewa ta zama abar misali ga sauran kasashen nahiyar Afirka. To sai dai Schröder bai yi magana game da karin taimakon kudi ga ATK ba, domin a na sa ganin a cikin shekarun da suka wuce kasashen biyu sun samu ci-gaba a huldarsu ta tattalin arziki.

A game da kasar Zimbabwe kuwa Schröder cewa yayi ko kadan baya goyon bayan manufofin gwamnatin shugaba Mugabe. Saboda haka Jamus na marawa matakan jan kunne da kungiyar tarayyar Turai EU ta dauka kan Zimbabwe. Shi ma a nasa bangaren, a karon farko Shugaba Mbeki ya soki lamirin shugaba Robert Mugabe, yana mai cewa a halin da ake ciki Zimbabwe ta tsunduma cikin matsalolin siyasa da na tattalin arziki. Mbeki ya kara da cewa ya fito fili ya fadawa shugaba Mugabe cewar matakan da ya ke dauka a kasarsa babban kuskure ne. Saboda haka ya yi kira ga gwamnati da ´yan adawa a Zimbabwe da su yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu, don samun sukunin warware matsalar wannan kasa.

A yau ne mista Schröder zai tashi zuwa kasar Ghana a matakin karshe na rangadin mako guda da yake kaiwa nahiyar Afirka.