Ziyarar shugaban Jamus a Najeriya
February 8, 2016Ziyarar ta Gauck dai wadda ta aiki ce ta fi mayar da hankali ne a babban birnin tarayyar kasar Abuja da ke arewaci da kuma Legas da ke kudanci, inda kuma shi ne cibiyar kasuwancin kasar. Gauck din dai na ziyara a kasar ne dai-dai lokacin da ake fuskantar kalubale na tsaro da kuma tsaurin tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen mai da kasar ke dogaro da shi don samun kudin shiga.
Tuni dai hukumomi a kasar suka nuna jin dadinsu dangane da wannan ziyara inda ministan yada labaranNajeriyar Alhaji Lai Muhammad ya ce wani yunkuri ne na amincewa da irin salon jagorancin shugaban Najeriyar Muhammdu Buhari, har ma ya ke cewar su na fatan ziyarar za ta kyautata danganta tsakanin kasashen biyu musamman ma ta fanin tattalin arziki.
Kungiyoyi fararen hula ciki kuwa har da ta masu fafutukar sako 'yan matan nan na Chibok sun yi maraba da wannan ziyara, inda shugabar kungiyar Aisha Yesufu ta ce su na fatan ziyarar ta Shugaba Gauck za ta yi tasiri kan yunkurin da suke yi na ganin an saki 'yan matan na Chibok, har ma suka bukaci da ya sanya baki kan wannan batu.
Wannan ziyara ta Gauck dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugabannin kasashe da dama ke cigaba da kara yaukaka dankon zumunci da gwamnatin ta Najeriya wadda yanzu haka ke fafutuka wajen gyara al'amura a kasar da kuma yunkuri na ganin an kawar da mummunar dabi'ar nan ta cin hanci da rashawa.