1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Westerwelle a Pakistan

January 8, 2011

Ministan harkokin wajen Jamus ya kai ziyarar rangadi Pakistan domin tattauna gudunmawar kasar wajen sulhunta rikicin Afghanistan

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle daga hannun dama da takwaransa na Pakistan Shah Mehmood Qureshi a birnin Islamabad.Hoto: picture-alliance/dpa

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya fara wata ziyara ta kwanaki biyu a ƙasar Pakistan inda zai gana da Firaministan ƙasar Yusuf Raza Gilani da Ministan harkokin waje Shah Meh-mood Qureshi da kuma wakilan jami'an sojin ƙasar a birnin Islamabad. Tattaunawar za ta maida hankali ne akan irin rawar da Pakistan za ta taka wajen sulhunta rikicin Afghanistan. Yankin arewacin Waziristan na ƙasar Pakistan wanda kuma ke maƙwabtaka da Afghanistan na zama maƙarfafar 'yan tawayen Taliban. Ministan harkokin wajen na Jamus Guido Westerwelle zai kuma kai ziyarar gani da ido aikin tallafi da Jamus ke gudanarwa a ɗaya daga cikin yankunan da ambaliyar ruwa ta yiwa ta'adi a bara.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita: Yahuza Sadissou Madobi