Afirka ta Kudu: An fara bincikar Zuma
July 15, 2019Talla
Al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu dai sun sa ido a akwatunan talabijin domin ganin da kuma sauraren jawaban da tsohon shugaban zai yi wa kwamitin domin kare kansa daga zargin.
Zargin cin hancin ne dai ya yi sanadiyyar yin awon gaba da kujerar mulkinsa, zargin kuma da ya sha karyatawa duk kuwa da wasu shaidu daga jami'an gwamnati na alakanta shi da yin sama da fadi da dukiyar kasar.