1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma ya ci alwashin daukaka kara

July 5, 2021

Hukuncin da kotun tsarin mulki a Afirka ta Kudu ta yanke kan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, na cigaba da tada kura. Lamari na baya- bayan nan shi ne fatali da tsohon shugaban da magoya bayansa su ka yi da hukuncin.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob ZumaHoto: Michele Spatarii/AP Photo/picture alliance

Dandazon matasa magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma yayin wani gangamin a garin Nkandla da ke lardin Kwa-Zulu Natal, mahaifar shugaba Jacob Zuma sun soki lamirin hukuncin da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yanke masa na zaman gidan kaso har tsawon watanni 15 bisa dalillan da kotun ta ce Mista Zuman ya ki mutunta ta.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob ZumaHoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Kotun dai ta bukaci tsohon shugaban da ya gurfana gaban wani kwamiti da ke bicike kan badakalar kudade da ake zargi Zuma ya handame a lokacin da yake jagorancin kasar lamarin da ya yi sanadiyar raba shi da madafun iko. Sai dai shugaban ya yi watsi da yunkurin tura shi gidan maza.

''Ba ni da bukatar bin umurnin kotun na zuwa gidan kaso duk da kasancewar babu wanda ya fi karfin doka, amma a shekaruna idan aka yi la'akari da halin da ake ciki na annobar Corona tamkar an yanke mani hukuncin kisa ke nan wanda tuni aka soke shi a kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu.''

Mataimakin babban jojin kasar mai shari'a Raymond Zondo wanda kuma shi ne shugaban kwamintin binciken ya ce kotu ta yi abin da ya dace.

''A tunaninmu wannan hukucin ya nuna karfin dimukaradiya a kasarmu tare da tabbatar da bin doka da ka'ida, haka zalika ya nuna karara cewa doka na sama da kowa kuma kowa dai-dai ya ke a gabanta.''

Magoya bayan Jacob Zuma sun yi alkawarin bashi kariyaHoto: Rogan Ward/REUTERS

Sai dai wasu daga cikin 'yan kasar masu goyon bayan shugaba Zuma sun tabbatar da cewa gwanin nasu bakin gwargwado mai biyayya ne ga dokokin kasa, kamar yadda babban sakataren jam'iyya mai mulki ta ANC kuma na hannun daman Zuma wanda aka dakatar na wani dan lokaci Elias Magashule ya yi tsokaci.

''Shugaba Zuma a ko wane lokaci mai biyayya ne ga dokokin kasa, domin kuwa yana daya daga cikin mutanen da suka 'yanto kasar nan. Duk ma wanda zaka ji yana kushe shi to bai san ko wanene Zuma ba, mutanen da muka sha fama lokacin yaki da wariyar launin fata. Mu mun san ko wanene Zuma.

Kwanaki biyar ne kachal aka bai wa Zuma da ya mika kansa a ofishin yan sanda na kauyensa ko na birnin Johannesburg, amma dai magoya bayansa sun ce ba za ta sabu ba, tare da yunkurin ba shi kariya ta musamman. Sibongiseni Bengu wani mai goyon bayan tsohon shugaban ne.

''Mu zamu hana a kama jagoranmu, duk wanda ke son kama shi to ya fara damu shi ne ma ya sa muka ja tunga nan, kuma muna nan duk sanda aka zo ko da nan da shekara ne.''

Kawo yanzu dai Jacob Zuma na fuskantar tuhume-tuhume guda 16 na karkatar da dukiyar al'umma gami da taushe kudin makamai.